Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya yi barazanar tsame Faransa daga Kungiyar Turai masu amfani da Visa daya

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy wanda yake ci gaba da yakin neman zaben shi wa’adi na biyu a zaben Shugabancin kasar da ke zuwa a watan gobe ya yi barazar tsame Faransa daga kungiyar kasashe 25 na Turai da basa amfani da Visa takardar izinin shiga kasashen waje.

Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa.
Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Shugaba Nicolas Sarkozy wanda yace kasar Faransa na fama da yawan baki, ya yi barazanar tsame faransa ne daga kungiyar kasashen Turai da suke shiga babu izini,

A cewar Sarkozy ya dace a yi wa tsarin da Kungiyar kasashen na Turai ke bi kwaskwarima, domin a taikata kwararar baki.

Shugaba Sarkozy yace kayayyakin da aka tanada na mutanen kasar, zasu kasance an yi masu yawa, saboda yadda wasu daga waje zasu amfana.

Yace cikin watanni 12 idan yaga lamarin bai gyaru ba, kasar Faransa na iya janyewa daga kungiyar kasashen Turai, 25 da ke bari a shiga da visa.

A wani gangamin makon jiya Shugaba Sarkozy, mai shekaru 56 ya furta cewa muddin bai ci zaben da ke tafe ba to kuwa shi da siyasa haihata-haihata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.