Faransa
Dan takarar Shugaban Faransa na jam'iyyar gurguzu ya soki matakin wasu shugabannin EU
Dan Takaran shugabancin kasar Faransa a Jam’iyar Gurguzu, Francois Hollande, ya soki wata yarjejeniya da aka ce shugabanin kasashen Turai masu akidar jari hujja sun kulla, dan kin ganawa da shi.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotanni sun ce, shugabanin kasahsen Birtaniya, Jamus, Italiya da Spain, sun yi alkawarin kaucewa Hollande, kan alkawarin da ya yi na sake duba yarjejeniyar kudaden kasashen Turai, idan ya samu nasarar zabe.
Hollande yac e, bai ji dadin rahotan ba, kuma Faransawa ne kawai zasu zabarwa kansu abinda suke so, ba wasu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu