Faransa
Hollande mai hamayya da Sarkozy yace wasu kasashen Turai basu ra’ayin shi
Dan Takarar shugabancin Faransa, a Jam’iyar Socialists, Francois Hollande, yace ba shi da niyar razana shugabanin jari hujjan kasashen Turai, duk da yake ya san cewar basu ra’ayin shugabancin shi sosai.
Wallafawa ranar:
Talla
Yayin da yake jawabi ga magoya bayan sa, Hollande yace, shi bai fito takara don ya razana su ba ne, duk da ya ke ya san cewar, manufofin sa sun sha ban ban da nasu.
Hollande yace, ya san cewa idan ya samu nasara dole zai yi aiki da su, amma ya dace su san matsayin sa, tun zubin farko.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu