Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun faransa ta tabbatar da 'yan takaran Shugaban kasa 10

Kotun Tsarin mulkin ta kasar Faransa ta wanke ‘yan takara 10 dake neman hawa kujerar Shugabancin kasar a zabe da za’ayi watan gobe na Afrilu.Kamar yadda Shugaban Kotun Kundin tsarin mulkin, Jean-Louis Debre na cewa ‘yan takaran 10 sun cika sharuddan da aka gindaya na kawo sunayen da sanya hannun mutane 500 ko wanne daga mazabarsa.

Yan takaran Shugaban kasar Faransa
Yan takaran Shugaban kasar Faransa
Talla

Ya ce za ayi zabe zagaye na farko ranar 22 ga watan gobe na Afrilu, sannan kuma a ranar 6 ga watan Mayu, a shiga zagaye na biyu tsakanin ‘yan takara biyu dake kan gaba.

'Yan takaran da aka wanke sun hada da Shugaba maici Nicolas Sarkozy na jamiyyar UMP mai mulki, sai Francois Hollande na jamiyyar Gurguzu, Sai Marine Le Pen na jamiyyar National Front. Akwai kuma Francois Bayrou na jamiyyar Modem.

Sauran ‘yan takaran sun hada da Jean-luc Melenchon na Left front, Eva Joly na jam'iyyar kare muhalli ta EELV, sai Nicolas Dupont-Aignan na DLR, akwai kuma Nathalie Arthaud na Trotskyist ta gwagwarmayar ma'aikata, sai Philippe Poutou, na sabuwar jamiyyar kyamar ‘yan jari hujja, yayinda Jacques Cheminade, ya kasance dan takara na Independent.

Bayanai daga masu auna wannan zabe dake gaba na nuna cewa Shugaba Nicolas Sarkozy na UMP da kuma Francois Hollande na jamiyyar Gurguzu, na kan-kan-kan, a zagaye na farko, kuma akwai alamun watakila idan aka kai zagaye na biyu, Hollande ya shawo kan wasu ‘yan takaran su mara masa baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.