Isa ga babban shafi
Faransa

Valls na fuskantar kaluble a zaben Faransa

Tsohon Firaministan Faransa Manuel Valls na ci gaba da fuskantar kalubale a yakin neman lashe zaben dan takarar jam’iyyar guruguzu ta Francois Hollande. 

Manuel Valls
Manuel Valls REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Mr.Valls na kokarin bin hanyoyin janyo ra’ayin faransawa domin ganin ya lashe zaben fitar da gwani a jam’iyyar da za a gudanar a ranar 22 ga wannan wata na Janairu.

Sai dai kuma ba shi da wani farin jini ga Faransawa kamar yadda farin jinin tsohon mai gidansa Francios Hollande ya dushe da har ya ce, ba zai nemi wa’adin shugabanci na biyu ba.

Valls dai na ci gaba shan kaye a kuri’un jin ra’ayin jama’a da aka gudanar, in da tsoffin ministocin masana’untu da ilimi Arnaud Montebourg da Benoit Hamon ke kan gaban shi da yawan kuri’u, sakamakon da ke nuna dayansu zai yi nasara a zaben fitar da gwanin a jam’iyyar ta Socialist.

Gangamin yakin neman zaben Valls da ya gudanar a karshen mako shi ya tabbatar da Faransawa ba sa ra’ayin shi saboda kalilan ne suka halarci gangamin.

Amma a hirarsa da kafar France 2, Mr. Vallas ya ce zai yi kokarin samun nasara kafin zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.