Isa ga babban shafi
Rasha

An gano musabbabin hatsarin jirgin Rasha

Masu binciken musababbin faruruwar hatsarin jirgin saman Rasha wanda ya kashe mutane 92, sun ce ga alama jirgin ya yi hatsari ne sakamakon samun tangardar inji.

Masu aikin agaji za su ci gaba da neman sauran gawarwakin fasinjojin jirgin sojin Rasha a teku a yau
Masu aikin agaji za su ci gaba da neman sauran gawarwakin fasinjojin jirgin sojin Rasha a teku a yau REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

A jiya Talata dai masu bincike suka sanar da gano bakin akwatin nadar bayanai a tekun Black Sea da wannan jirgin ya fada a ranar Lahadin da ta gabata bayan ya tashi daga Rasha zuwa Syria.

Majiyoyi daga Rasha sun bayyana cewa, a yau Laraba za a ci gaba da gudanar da bincike a tekun da nufin tsamo sauran gawarwakin fasinjojin jirgin da kuma sauran buraguzansa.

Tuni masu aikin agaji na Rasha suka tsamo gawarwakin mutane 12 tare da sassan jikin dan adam fiye da150 a jiya, in da aka aike da su birnin Moscow don gudanar da gwajin kwayar halitta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.