Isa ga babban shafi

Ana bincike kan akwatin jirgin Rasha a Moscow

Jami’an agajin Rasha sun gano bakin akwatin jirgin saman sojin kasar da ya yi hatsari a tekun Black Sea dauke da mutane 92, yayin da kwararru ke gudanar da bincike kan akwatin a birnin Moscow. 

Jami'an agajin gaggawa na Rasha da suka gano bakin akwatin jirgin saman sojin kasar da ya yi hatsari a ranar Lahadi
Jami'an agajin gaggawa na Rasha da suka gano bakin akwatin jirgin saman sojin kasar da ya yi hatsari a ranar Lahadi (Reuters)
Talla

Ma’aikatar tsaron Rasha ta bayyana cewa, a safiyar yau Talata ne aka gano bakin akwatin da ake sa ran zai bada bayani game da yadda jirgin sojin samfurin Tu-154 ya yi hatsari a tekun bayan ya baro yankin Sochi zuwa Latakia na Syria a ranar Lahadin da ta gabata.

Rahotanni sun ce, akwatin ba ta lalace ba, yayin da kuma kwararru ke ci gaba da gudanar da bincike a birnin Moscow kan bayanan da akwatin ya nada gabanin aukuwar hatsarin.

Tuni dai masu gudanar da binciken suka bayyana cewa, babu alamar ta’addanci ne ya yi sanadiyar hatsarin jirgin da ke dauke da sojoji da wasu fitattun mawakan goge da kuma ‘yan jaridu.

An gano bakin akwatin ne a lokacin da masu aikin agaji ke kokarin tsamo gawarwakin fasinjoji da kuma buraguzan jirgin a teku.

Ma’aikar tsaron Rasha ta ce, an kuma gano gawarwakin mutane 12 da kuma sassan jikin dan Adam har guda 156, yayin da kuma ake gudanar da gwajin kwayar halitta kan gawarwakin da sassan jikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.