Isa ga babban shafi
Rasha

An gano akwatin nadar bayanan jirgin Rasha da ya fadi a teku

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce an gano akwatin jirgin saman sojin kasar da ya fadi dauke da mutane 92 ne a tekun Black Sea a ranar Lahadi kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar ya ruwaito.

An gano tarkacen jirgin sojin Rasha da ya fadi a tekun black sea
An gano tarkacen jirgin sojin Rasha da ya fadi a tekun black sea (Reuters)
Talla

Rahotanni sun ce an dauki akwatin zuwa birnin Moscow domin gudanar da bincike tare da tatsar bayanan da ke cikinsa.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce an yi nasarar tsamo gawarwakin mutane 12 da kuma tarkacen jirgin da dama a cikin tekun da jirgin ya fadi.

Jirgin sojin kasar mai suna Tu-154 jet ya fadi ne dauke da sojojin Rasha 60 akan hanyarsu zuwa Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.