"Babu kasar da ta kai Rasha karfin soji"-Putin
Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin yace babu wata abokiyar gabar Rasha yau dake da karfin sojin da zata iya fuskantar kasar sa.
Wallafawa ranar:
Yayin da yake jawabi karshen shekara ga al’ummar kasar, Putin yace babu tantama kasancewar a halin yanzu babu wata kasar da ta kai Rasha karfin soji daga cikin abokan gabarta.
Shugaba Putin yace a shirye Rasha take, ta gaggauta murkushe duk wata kasa da ta yi mata barazana, yayin da yace bunkasa makamin nukiliya shi ne abinda kasar zata mayar da hankali kai a sabuwar shekara.
Putin ya kuma yabawa sojojin kasar kan rawar da suke takawa a yakin Syria, musamman taimakawa sojin gwamnatin kasar da suka yi wajen kwato dukkanin birnin Aleppo daga ‘yan tawayen kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu