Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Obama ya zargi Putin kan kutsen zaben Amurka

Shugaban Amurka mai barin gado, Barack Obama ya zargi takwaransa na Rasha, Vladmir Putin da daukan nauyin kutsen da Amurka ta ce, an yi mata a zaben shugabancin kasar da ta gudanar.

Shugaban Rasha, Vladmir Putin na Rasha da Barack Obama na Amurka
Shugaban Rasha, Vladmir Putin na Rasha da Barack Obama na Amurka REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Hukumar leken asirin Amurka ta ce, an yi kutsen ne da nufin taikawa Donald Trump na jami’iyyar Republican lashe zaben na ranar 8 ga watan Nuwamba da ya wuce.

Mr. Obama wanda ke magana gabanin tafiya hutu tare da iyalansa a jihar Hawaii, ya ce, sabanin da ke tsakanin Democrat da Republican ne, ya bai wa Rasha damar haddasa musu fitina.

Rahoton hukumar ta CIA ya ce, Rasha ta yi kustsen ne a sakwannin Imel na kwamitin jam’iyyar Democrat da kuma na shugaban yakin neman zaben Hillary Clinton, wato John Podesta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.