Isa ga babban shafi
Amurka

Babu wata shedar magudi a zaben Amurka

Fadar Shugaban Amurka ta yi watsi da zargin da shugaban kasar mai jiran gado Donald Trump ya yi cewar miliyoyin ‘yan kasar sun kada kuri’a ta hanyar da ba ta dace ba a zaben shugaban kasa da ya kada Hillary Clinton a 8 ga Nuwamba.

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst/File Photo
Talla

Bangarorin Masana da Jami’an zabe sun yi watsi da zargin na Trump yayin da ake kokarin sake kidayar kuri’u a wasu manyan jihohin Amurka.

Mai Magana da yawun fadar shugaban, Josh Ernest ya ce ya zuwa yanzu babu wata kwakkwarar shaidar da Trump ya gabatar da za ta tabbatar da zargin.

Trump dai ya lashe zaben shugaban kasar ne da rinjayen kuri’un wakilai akan abokiyar hamayyar shi Hillary Clinton da ta samu rinjayen kuri’un jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.