Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ba zai binciki Clinton ba

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya yi watsi da barazanar hukunta abokiyar hammayar shi Hillary Clinton kamar yadda ya yi alkawali a lokacin da suke yakin neman zabe.

Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat da Donald Trump na Republican da ya doke ta a zaben Amurka
Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat da Donald Trump na Republican da ya doke ta a zaben Amurka REUTERS/Mike Segar/File Photo
Talla

Trump ya ce ba zai ci gaba da binciken Clinton ba domin yin hakan zai kara raba hadin kan ‘Yan kasa.

Shugaban yakin neman zaben shugaban na Amurka mai jiran gado Kellyanne Conway, ya ce daukacin ‘Yan majalisar jam’iyyar Republican, sun ajiye aniyarsu ta bincikar Clinton kan sakwanninta na imel.

Babu dai laifi da aka kama Clinton da shi bayan hukumar tsaro ta FBI ta gudanar da bincike akan sakwanninta na Imel na kashin kanta da ta yi amfani a lokacin tana sakatariyar harakokin wajen Amurka.

Sai dai akwai magoya bayan Trump da ke son zababben shugaban ya cika alkawalin da ya dauka na bincikar Hillary Clinton.

Amma Trump ya ce ba ya son ya sake muzanta gidan Clinton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.