Isa ga babban shafi
Ingila

An bankado zargin lalata da kananan yara kashi 350 a Ingila

Hukumar ‘yan sanda ta Birtaniya, ta ce, kimanin mutane 350 ne suka shigar da kara kan lalatar da masu horar da kungiyoyin kwallon kafa suka yi da su, a lokacin da suke kananan yara

Shugaban Hukumar 'yan sandan Birtaniya Simon Bailey
Shugaban Hukumar 'yan sandan Birtaniya Simon Bailey
Talla

Shugaban hukumar ‘yan sandan Ingila, Kwanstebul Simon Bailey ya ce, suna aiki tukuru tare da hukumar kwallon kafa ta kasar don ganin cewa, an dauki matakin da ya dace cikin tsari, lura da yawan adadin ‘yan wasan da aka ci zarafinsu.

A satin da ya gabata, Andy Woodward, mai shekaru 43, da ya buga wasa a gasar kwallon Ingila ajin da ke kasa da gasar Premier League, ya shaidawa jaridar the Guardian ta kasar yadda ya ce aka kassara masa rayuwa, saboda yadda mai horar da kungiyar da yake ciki a waccan lokacin ya ci zarafinsa.

Biyo bayan wannan bankada da Woodward yayi, ya sanya wasu tsaffin ‘yan wasa 20 fitowa su bayyana yadda suka fuskanci cin zarafin da ya faru da su a tsakanin shekarun 1970-1990.

A ranar Talatar da ta gabata, aka gabatar da kararraki 8, kan Barry Bennell mai shekaru 62 game da zarginsa da ake, na yin lalata da wani karamin yaro mai shekaru 14, a lokacin da ya horar da kungiyoyin Crewe Alexandra da kuma Manchester City.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.