Isa ga babban shafi
Wasanni

An haramtawa 'yan wasan Ingila shakatawa yayin wasanni

Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Ingila, ta haramtawa ‘yan wasan kasar fita shakatawa ko wuraren sheke aya, muddin suna wakiltar kasar wajen buga wasanni.

Kaftin din tawagar 'yan wasan Ingila Wayne Rooney
Kaftin din tawagar 'yan wasan Ingila Wayne Rooney Reuters / Stefan Wermuth Livepic
Talla

Hukumar FA ta Ingila ta dauki wannan mataki ne saboda bayanan da ta samu na cewa, ‘yan wasan ingila sun fice zuwa holewa a daren ranar Asabar data gabata, bayan samun nasara a wasan da suka yi da kasar Scotland da kwallaye 3-0, kwanaki uku bayan wannan shakatawa suka tashi 2-2 a wasan sada zumunci da suka yi da kasar Spain.

A wannan wasa dai da fari Ingila ce ta zurawa Spain kwallaye 2 tare da samun maki mai yawa na rike kwallo amma daga baya sai labari ya canza.

Hukumar kwallon kafar Ingila na ganin ba shakka ‘yan wasanta sun samu raguwar karsashin da suke da shi ne sakamakon shantakewar da suka yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.