Isa ga babban shafi
Wasanni

An bukaci a daure Eto'o na shekaru 10

Masu gabatar da karar a Spain sun bukaci a daure tsohon dan wasan Barcelona Samuel Eto’o dan kasar Kamaru, shekaru 10 a gidan yari, da kuma biyan tarar kudin da ya kai Dala miliyan 19.

Dan wasan Kamaru Samuel Eto'o
Dan wasan Kamaru Samuel Eto'o REUTERS/Andres Stapff
Talla

Bukatar hukunta Eto’o ya biyo bayan zargin da ake masa da kafa wasu kamfanomin domin kaucewa biyan haraji tsawon lokacin da ya dauka yana taka leda a kungiyar ta La Liga.

Tuhumar da ake yiwa dan wasan ta fi mayar da hankali kan kamfanin da ya kafa a shekarar 2006, yana aikata Coge, tare da boye kudadden da yawansu ya kai euro miliyan 4 na haraji.

Eto’o da ke wasa a kungiyar Antalyaspor da ke Turkiya a cewar masu shigar da karar ya zama dole ya fuskanci shari’ar.

Zargin da ake wa Eto’o na zuwa ne, yayin da a yanzu haka Lionel Messi da Neymar fitattun ‘yan wasan Barcelona ke fuskantar irin wannan tuhuma kan batun da ya shafi haraji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.