Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta ware kudaden inganta aikin ‘Yan sanda

Gwamantin Faransa ta amince ta kashe karin wasu kudade da yawansu ya kai yuro milyan 250 domin inganta aikin dan sanda a kasar, a daidai loakcin da ‘yan sanda suka share tsawon makwanni suna zanga-zanga.

Zanga Zangar 'Yan sandan Faransa
Zanga Zangar 'Yan sandan Faransa REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Za a yi amfani da kudaden ne domin sayen rigunan kariya daga harsashe har guda dubu 21, tare da rage wa ‘yan sanda lokutan aiki kamar yadda suka bukata.

Bayan ganawa tsakanin wakilan ‘yan sandan da kuma shugaban kasar François Hollande, Ministan cikin gidan kasar Bernard Cazeneuve ya ce ya zaman wajibi a kara yawan kudaden da a ke kashewa domin samar wa ‘yan sanda kayan aiki.

“Dole ne mu aiwatar da gagarumin shiri na inganta yadda suke gudanar da ayyukansu sakamakon halin da duniya ke ciki na kalubale ta fannin tsaro”.

Cazeneuve ya ce za su ci gaba da tattaunawa da manyan jami’ai ‘yan sandan, domin sanin fannonin da ‘yan sandan ke bukatar taimako a cikin gaggawa.

Ministan ya ce za su fara aiwatar da shirin inganta ayyukan ‘Yan sandan a cikin tsanaki kuma a gaggauce.

Wannan dai na zuwa ne bayan ‘Yan sandan a Faransa sun kaddamar da zanga-zanga domin nuna adawa da hare haren da ake kai musu da kuma kalubalen da suke fuskanta na karancin kayan aiki da tilasta masu zarce lokacin aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.