Isa ga babban shafi
Faransa

Yawan marasa aikin yi a kasar Faransa sun ragu

Yawan marasa aikin yi a kasar Fransa sun ragu a watan Satumba da ya gabata irinsa na farko tun shekarar 1996, shekaru 20 kenan da suka gabata, labari da ya faranta rai ga mahukuntan gwamnatin gurguzun kasar.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Charles Platiau
Talla

Yawan marasa aikin yin da ke rubuce a ma’aikatar samar da ayyukan yi sun ragu da mutane dubu 66,300 wanda rabon da a samu haka shekaru 20 ke nan da suka gabata, adadin da ke wakiltar faransawa miliyan 3.4, kamar yadda ofishin ma’aikatar kwadagon kasar ta sanar.

Raguwar da aka samu kuma na wakiltar 1,9%, adadi mafi yawa da aka taba gani a kasar tun a watan Nuwamban 2000.

Sakamakon da ma’aikatar samar da ayyukan yi ta Pôle emploi, ta bayar ya nuna cewa yanzu haka mutane miliyan 3.5 ne aka raba da zaman kashe wando tun janairun 2015. A yayinda aka samu ragin marasa aikin yi da mutane dubu 90 tun farkon shekara bana.

Raguwar rashin ayyukan yi da ya fi shafar matasa a kasar ta Faransa, ya kai 5,3% na masu neman aikin irinsa mafi yin kasa a cikin shekaru 25 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.