Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta jaddada kudirinta kan dokar kwadago

Shugaban Faransa Francois Hollande ya bayyana cewa, har yanzu gwamnatinsa ba ta yi nasara ba a kan yaki da matsalar rashin aikin yi, yayin da ya lashi takobin tabbatar da kudirinsa na kawo sauye- sauye a harkar kwadago a kasar.

Masu zanga zangar adawa da shirin gwamnatin Faransa a birnin Nantes na Faransa a wannan Talata
Masu zanga zangar adawa da shirin gwamnatin Faransa a birnin Nantes na Faransa a wannan Talata REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Yunkurin samar da sauye sauyen dai ya haifar da zanga zangar watanni biyu a titunan kasar, amma hakan bai tilasta wa gwamnatin janye shirinta ba.

A wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Europe 1, shugaba Hollande ya ce, ba zai janye daga kudirinsa saboda gwamnatoci da dama da suka shude sun janye matakan da suka dauka saboda yadda jama'a suka nuna adawarsu akai.

Hollande ya ce, ya gwammace al’ummar kasar su yi tutiya da shugaban kasa da ya yi mu su aiki, amma ba shugaban da bai yi komai ba a kan karagar mulki.

Tuni dai direbobin manyan motoci suka datse hanyoyi a yankin yammacin Faransa a wannan Talata domin fara sabuwar zanga zangar adawa da shirin na gwamnatin.

Gwamnatin dai ta yi ikirarin cewa, shirin zai saukake gudanar da harkar kwadago a kasar yayin da ‘yan adawa suka bayyana shakkunsu tare da fadin cewa , hakan zai jefa dimbin jama’a cikin rashin aikin yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.