Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar Faransa na nazari kan dokar kwadago

Majalisar dokokin Faransa ta fara nazari kan shirin gwamnatin kasar na samar da sauye sauye a dokar kwadago ta kasar a wannan Talata.

A yau Talata majalisar Faransa ke nazari kan shirin dokar kwadago ta kasar
A yau Talata majalisar Faransa ke nazari kan shirin dokar kwadago ta kasar REUTERS/Charles Platiau
Talla

Wannan shirin dai ya haifar zanga zanga ta tsawon watanni biyu a titunan kasar, abinda ya rikide ya koma tarzoma tsakanin jami’an ‘yan sanda da fararen hula.

A yayin da ya rage watanni 12 a gudanar da zaben shugabancin kasar, ana ganin watakila, irin wannan dokar ce za ta zama ta karshe da gwamnatin Socialist ta Francois Hollande za ta gabatar.

Ana sa ran kungiyoyin kwadago da na dalibai za su gudanar da zanga zanga a wannan Talata a harabar majalisar dokokin, a dai dai lokacin da mambobin majalisar ke nazari kan shirin dokar.

Tuni dai gwamnatin Hollande ta sauya wasu bangarori a shirin dokar bayan zanga zangar da aka gudanar, amma duk da haka, kungiyoyin fararen hula ba su amince da tsarin ba, inda suka bukaci a janye shi baki daya.

Wasu daga cikin abubuwan da dokar ta kunsa, sun hada da matakan koran ma’aikata cikin kankanin lokaci, abinda ya fi daga wa ‘yan kasar hankali.

Sannan kuma tsarin zai bai wa kamfanoni damar sallamar ma’aikatansu musamman idan kamfanonin na samun asara a Faransa, ko da kuwa rassansa da ke kasashen ketare na samun riba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.