Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa: ‘Yan sanda sun yi zanga-zangar ba-zata a Paris

‘Yan sanda a Faransa sun kaddamar da wata zanga-zanga domin nuna adawa da hare haren da ake kai musu da kuma kalubalen da suke fuskanta na karancin kayan aiki da tilasta masu zarce lokacin aiki.

'Yan sanda sama da 500 suka shiga zanga-zanga a Champs-Elysees a Paris
'Yan sanda sama da 500 suka shiga zanga-zanga a Champs-Elysees a Paris AFP
Talla

Tun a daren jiya ‘Yan sandan suka kaddamar da zanga-zangar inda suka mamaye dandalin Champs Elysee a Paris.

Daruruwan ‘Yan sandan  sun mamaye dandalin Champs Elysse da motocinsu tare da yayata dandalin da jiniya da kunna fitillun mota.

‘Yan sandan da ke fuskantar matsin lamba sakamakon hare haren ta’addanci da aka kai a Paris, sun ce suna fuskantar karancin kayan aiki kuma suna zarce lokacin da ya kamata ace sun tashi aiki.

Wani dan sanda daga cikin masu zanga-zangar da aka zanta da shi ya ce sun yanke shawarar kaddamar da zanga-zangar ne ba tare samun goyon bayan kungiyarsu ba.

A cewar shi aikin dan sanda na neman ya gagare su.

A kwanan baya dai kungiyar ‘yan sandan ta koka kan hatsarin gudanar da aiki a wani yanki na kudancin Paris inda kowa ke tsoron zuwa musamman bayan kisan wasu ‘yan sanda biyu a wani harin bom da aka kai musu.

A cikin sanarwar da ya fitar babban daraktan hukumar yan sandan na Faransa Jean-Marc Falcone ya yi allawadai da zanga-zangar, yana mai cewa dan sanda bai kamata ya ketare hakkin da ya rataya akanshi ba.

Sannan Mista Falcone ya ce za a kaddamar da bincike akan gano wadanda suka jagoranci boren na ‘yan sanda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.