Isa ga babban shafi
Venezuela

An dakatar da shirin kada kuri'ar jin ra'ayi a Venezuela

Jami’an hukumar shirya zaben kasar Venezuela, sun dakatar da shirin kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a, a kokarin ganin an kawo karshen gwamnatin shugaban kasar Nicolas Maduro.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro
Talla

Wannan matakin dai ya zama koma baya ga ‘yan adawa a kasar, wadanda ke fafutukar ganin shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa, a cewarsu saboda ya gaza wajen warware matsalar tattalin arzikin kasar.

Matakin dakatar da shirya kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ya zo ne bayan haramta sanya hannun da miliyoyin ‘yan adawa a Venezuela, na bukatar kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kotuna da dama a kasar suka yi.

Zalika tsohon dan takarar shugabancin Venezuela Henrique Capriles, ya yi watsi da umurnin wata babbar kotun kasar, na hana shi fita daga kasar tare da wasu manyan ‘yan adawa 7.

‘Yan adawa a Venezuela sun dora alhakin koma bayan tattalin arziki da kasar ke fama da shi kan Shugaba Maduro, a cewarsu shugaban ya kasa kawo karshen matsalar hauhawar farashin kayan abinci, tsadar magani da kuma yawaitar aikata laifuka a kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.