Isa ga babban shafi
Venezuela

Nicolas Maduro na cikin matsin lamba

‘Yan adawa na ci gaba da yi wa shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro matsin lamba, domin tilasata masa amincewa a gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a domin fayyace makomarsa.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro Fuente: Reuters.
Talla

‘Yan adawar wadanda ke da rinjaye a zauren majalisar dokoki, sun hana wa shugaban kasar yin amfani da dokar ta baci, inda kuma suka bukaci al’ummar kasar da su ci gaba da tarzoma sai zuwa lokacin da aka gudanar da kuri’ar raba gardamar ko kuma ya sauka daga karagar mulki.

Sojoji kusan rabin milyan ne za su fara wani atisaye a wannan juma’a a kasar a dai-dai lokacin da kasar ke fama da rikicin siyasa.

Yanzu haka dai kasashen duniya sun yi tayin shiga tsakani domin fara tattaunawa tsakanin shugaba Nicolas Maduro da kuma ‘yan hamayya da ke neman ya sauka daga mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.