Isa ga babban shafi
Venezuela

Ana zanga-zangar adawa da Maduro a Venezuela

‘Yan adawa a Venezuela sun kaddamar da zanga zanga a sassan kasar domin neman a gudanar da kuri’ar raba gardama da za ta tantance makomar shugabancin Nicolas Maduro.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro.
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro. Fuente: Reuters.
Talla

‘Yan adawar na gudanar da zanga-zangar ne duk da gwamnatin Maduro ta kafa dokar ta-baci domin dakile aniyarsu ta ganin bayan shi.

Zanga-zangar ta kasance babban kalubale ga gwamnatin Venezuela duk da kafa dokar ta baci a kasar.

‘Yan adawar sun mamaye Caracas babban birnin Venezuela da wasu manyan biranen kasar suna masu yin kira ga gwamnati ta amince a gudanar da kuri’ar raba gardama kan makomar shugaban kasar Nicolas Maduro.

Mutanen Venezuela kusan miliyan biyu suka sanya hannu kan bukatar ganin an tsige shugaban.

A ranar Litinin ne gwamnatin Maduro ta kafa dokar ta baci ta tsawon watanni biyu domin maganin adawar da ya ke fuskanta da yace barazana ne ga tsaron kasa.

Amma shugabannin adawa a kasar sun yi watsi da dokar wacce suka ce karan tsaye ne ga mulkin dimokuradiya.

‘Yan adawar sun yi kira ga magoya bayansu su bijirewwa dokar tare yin kira ga rundunar sojin kasar ta fito ta fayyace matsayinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.