Isa ga babban shafi
Venezuela

Maduro ya kira bore a Venezuela idan an kawar da shi

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bukaci magoya bayansa da su yi tawaye tare da shiga yajin aiki, matukar ‘yan adawa sun yi nasarar kawar da shi daga karagar mulki a zaben raba gardamar da suke so a gudanar nan da karshen shekarar 2016.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro.
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro. REUTERS/Miraflores Palace
Talla

Shugaba Maduro ya bayyana haka ne ga magoya banyansa a jawabin bikin ranar ma’aikata da ya gabatar a fadarsa a Lahadi, yana mai umurtarsu shiga yajin aiki, da yin tawaye idan ‘yan adawar sun kawar da shi daga madafun iko.

‘Yan adawan su fara shirin kawar da shi , inda za su gabatar da sanya hannu da ya ninka dubu 200 har sau 10, adadin da ake bukata kafin hukumar zabe ta amince da fara shirin gudanar da zaben raba gardamar domin kawar da Maduro.

Sai dai shugaba Maduro ya ce zaben raba gardama ba wajibi ba ne kamar na shugaban kasa wanda za a gudanar a shekara ta 2018.

Wannan na zuwa ne a yayin da dimbin jama’ar kasar Venezuela ke caccakar Maduro saboda matsalar tattalin arzikin da ta addabi kasar.

Shugaban ya lashi takobin kare kujerarsa duk da matsalolin da kasar ke fuskanta, abin da ya sa wasu suka gudanar da zanga-zanga da ya hada da wadda aka gudanar saboda katsewar wutar lantarki na tsawon sa’oi hudu a kowace rana.

Wata kuri’ar jin ra’ayi ta kwanan nan da aka gudanar a kasar, ta nuna cewa, sama da kashi biyu cikin uku na al’ummar kasar na goyon bayan kawar da Maduro daga karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.