Isa ga babban shafi
Jarida

‘Yancin ‘Yan Jarida ya tabarbare a duniya

Kungiyar da ke sa ido kan aikin jarida a duniya ta sanar da cewar ‘yancin gudanar da aikin jarida ya tabarbare a shekarar 2015 musamman a kasashen da ke Yankin kudanci da Latin Amurka.

Jaridun Faransa
Jaridun Faransa THOMAS OLIVA / AFP
Talla

Rahotan hukumar ya yi nazari kan kasashe 180 na duniya inda ya nuna yadda shugabanin wasu kasashe ke amfani da karfin mulki wajen katsalandan kan yadda ‘yan jaridu ke gudanar da ayyukansu da kuma yadda ake kai wa ‘yan jaridun hari.

Rahotan ya bayyana kasashen Venezuela da Ecuador da Honduras da Columbia da kuma Brazil a matsayin wadanda hukumomi ke musgunawa ‘yan jaridu.

Rahotan ya kuma sanya kasashen da ke matakan karshe a jerin masu ‘yancin gudanar da aikin jarida da suka kunshi China a matsayi na 176, Syria a matsayi na 177, sai kuma Koriya ta Arewa na 179.

Kasar Finland ke matsayin farko wajen walwalar gudanar da aikin, sai Netherland a matsayi na biyu sai kuma Norway a matsayi na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.