Isa ga babban shafi
Venezuela

Yan adawa na gangamin tilastawa shugaba Maduro sauka daga mulki

Madugun adawa na kasar Venezuela Henrique Capriles ya ce dole soja su yi zabi tsakanin kundin tsarin mulkin kasar ko kuma shugaban kasar Nicolas Maduro.

Gangamin tilastawa  shugaba Nicholas Maduro sauka daga mulki.
Gangamin tilastawa shugaba Nicholas Maduro sauka daga mulki. ©REUTERS/Marco Bello
Talla

Madugun adawan na Magana ne a yayin tattaunawa da manema labarai, bayan da shugaban kasar ya ayyana dokar ta baci, da karawa soja da ‘yan sanda sabon karfi fiye da na da.

A yau ne dai ‘yan adawan kasar ke shirin yin fito na fito da jamian tsaro, domin yin gangamin tilastawa shugaban kasar Nicholas Maduro sauka daga iko.

Shugaba Maduro dai ya kafa dokar ta bacci sakamakon barkewar rikicin siyasa da na tattalin arziki a kasar inda tuni ya kare matakin a matsayin wata dama yakar masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.