'Yan adawa sun sake kaddamar da zanga zanga a Venezuela
Yan adawa a kasar Venezuela sun sake kaddamar da sabuwar zanga zanga domin tilastawa shugaban kasar Nicolas maduro bawa jama'ar kasar damar kada kuri’ar sauke shi daga mukaminsa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sabuwar zanga zangar ta zo sati guda bayan gudanar da makamanciyarta a babban birnin kasar Caracas.
Magoya bayan gamayyar jam’iyyun adawa na MUD sun yi ikirarin cewa dole Maduro ya sauka da mukaminsa, saboda gazawarsa karara wajen magance tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
Venezuela na fama da karancin abinci da magunguna a asibitoci.
Har yanzu dai ‘yan adawa a kasar suna cigaba da kokawa bisa yadda suka ce jami’an tsaro suna kame magoya bayansu, musamman a zanga zangar da ta gudana a ranar Alhamis din da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu