Isa ga babban shafi
Haiti-MDD

Al'ummar Haiti na bukatar agajin gaggawa

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa kasar Haiti da kayyayakin agaji ganin halin kuncin da al’ummar kasar suka sami kansu sakamakon barnar da guguwar Mathew ta haifar.

Ban Ki-Moon a Ziyarar da ya kai kasar Haiti bayan aukuwar guguwar Mathew
Ban Ki-Moon a Ziyarar da ya kai kasar Haiti bayan aukuwar guguwar Mathew REUTERS/Andres Martinez Casares
Talla

Mr Ban dai ya kai ziyara kasar inda ya ganewa idanunsa barnar da guguwar ta haifar, ya kuma yi alkawarin tallafawa Haiti kafin daga bisani ya yi kira ga sauran kasashen duniya da su bi sahu don taimaka al’umma da agaji.

Mutane fiye da miliyan daya ne ke bukatar agajin gaggawa yayin da ake kokarin hana barkewar cutar kwallera a kasar.

Munmunar Guguwar da aka yiwa lakani da Mathewa ta yi sanadiyar mutuwar mutane 900 a Haiti.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.