Isa ga babban shafi
Israel-Palestine-UN

Ban Ki-moon zai Gabatarwa MDD Halin da ake Ciki Tsakanin Israela da Palestinawa

Yau ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ke yiwa Komitin sulhu na Majalisar bayanai gameda tashe-tashen hankula na baya-bayan nan tsakanin Israela da Falestinawa.

Sakatare Janar na MDD Ban Kimoon , tare da Shugaba Netanyahu
Sakatare Janar na MDD Ban Kimoon , tare da Shugaba Netanyahu AFP/AFP
Talla

Ban Ki-moon ya riga ya gana da Fira Ministan Israela Benjamin Netanyahu, bayan ya gana da Shugaban Falestinawa Mahmud Abbas inda ya gargade su da su guji kazancewar rikici a yankin nasu.

Ya roki bangarorin biyu dasu yi tattalin zaman lafiya.

Ganin yadda rikici tsakanin Israela da Falestinawa ke kara ta'azzara Sakataren waje na Amirka John Kerry cikin wannan makon zai gana da Benjamin Netanyahu da kuma jagoran Falestinawa Mahmud Abbas da Sarki Abdallah na Jordan duk dai domin neman warware rikici tsakanin Israela da Falestinawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.