Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta rage wa tsoffin shugabanninta kudaden gata

Faransa ta kaddamar da sabuwar doka da ke rage yawan hakkokin da ake bai wa tsoffin shugabannin kasar bayan sauka daga aiki, kamar yadda shugaba Francois Hollande ya bukata.

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande REUTERS/Ian Langsdon
Talla

Wannan sabon sauyi da aka samu a Faransa, ya zo ne daidai lokacin da ‘yan siyasa suka dau harama domin kintsawa zaben shugabancin kasa da za a gudanar nan da watanni shida masu zuwa.

Wasu daga cikin abubuwan da dokar ta kunsa sun hada da rage yawan jami’an da ke wa shugaban da ya share shekaru biyar kan karagar mulki hidima daga mutane bakwai zuwa uku.

Har ila yau akwai wasu sauran hakkoki da za a ragewa tsoffin shugabannin kasar, da ke fara aiki shekaru 10 bayan saukar shugaba daga mukaminsa. Faransa dai na kashe sama da kudi yuro milyan 10 domin daukar dawainiyar tsoffin shugabannin kasar.

Sai dai ba kowane tsohon shugaba ne sabuwar dokar za ta shafa ba, illa wadanda aka rantsar kafin ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2012, wanda hakan ke nuna cewa dokar za ta fara aiki akan shugaba mai-ci Francois Hollande da zarar ya sauka daga mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.