Isa ga babban shafi
Faransa

Za'a hukunta sojojin Faransa saboda cin zarafin dan 'adam

Hukumar ladabtar da sojojin kasar Faransa ta fara nazari kan korafin da aka shigar, kan wasu sojoji biyar da aka samu da laifin cin zarafin dan Adam a lokacin da suke aikin samar da zaman lafiya a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya a 2014.

Talla

Sojojin biyar sun yi ma wani dan kasuwa ne da ya tsere da kudinsu dukan tsiya.

An dade ana zargin sojojin kasar ta Faransa da ake aikawa aikin samar da zaman lafiya da wuce gona da iri, ta hanyar cin zarafin dan Adam da lalata da kanan yara.

A watan Maris na 2014 lokacin da rundunar sojojin RIMA ta kammala aikinta ne sojojin suka ba wani dan kasuwa kudi ya sayo musu tsaraba shi kuma ya tsere da kudin da suka kama shi ne suka masa dukan kawo wuka har sai da wani babbansu ya cece shi.

Dama dai ana zargin wasu sojojin kasar ta faransa da laifin yin lalata da kanana yara, da cin zarafin dan Adam a lokacin da ake tura su ayyukan tabbatar da tsaro a wuraren da ake samun matsalar tsaro.

Sojojin Biyar na iya fuskantar hukunci da suka hada da ragin matsayi zuwa kora saboda laifukan da aka same su dake zubar da kima da mutuncin dakarun kasar da ma na kasar ita kanta.

Za a bayyana hukuncin nan da watanni hudu masu zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.