Isa ga babban shafi
Italiya

Italiya ta kafa dokar ta-baci

Gwamnatin Kasar Italiya ta kafa dokar ta-baci sakamakon girgizar kasar da ta lakume rayukan mutane 250, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da gudanar da ayyukansu domin ceto masu saurin numfashi.

Ana ci gaba da aikin ceto mutane a Amatrice da girgizan kasa ta shafa a Italiya
Ana ci gaba da aikin ceto mutane a Amatrice da girgizan kasa ta shafa a Italiya REUTERS/Stefano Rellandini
Talla

An sake samun wata girgizan kasa mai karfin maki 4.7 a yau Juma’a.

Rahotanni sun ce akasarin wadanda suka mutu sun fito ne daga Amatrice inda aka samu gawarwaki 193.

Wata mata mai suna Rita Rosine ‘yar shekaru 63 da ta rasa ‘yar uwarta mai shekaru 75 ta bayyana illar girgizar kasar a matsayin abin da ya zarce yaki.

Firaministan Italiya Matteo Renzi ya yi alkawalin ware kudi kusan Dala miliyan hamsin domin sake gina yankin da bala’in girgizan kasar ya shafa.

Rahotanni sun ce sama da mutane 400 suka samu rauni a girgizan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.