Isa ga babban shafi
Italiya

Sama da Mutane 2,500 sun rasa gidajensu a birnin Norcia

Wata girgizar kasa da ta auku a sanyin safiyar Laraba a birnin Norcia da ke yankin Umbria na kasar Italiya ta ta yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 73 tare da rusa kauyuka a kalla 17 a yankin. 

Girgizar kasa ta lalata hanyoyi a Norcia da ke Italiya
Girgizar kasa ta lalata hanyoyi a Norcia da ke Italiya REUTERS/Kyodo
Talla

Kawo yanzu ma’aikatan ceto a kasar Italy sun ce bayan mutuwar mutane da dama ana cigaba da neman wasu daruruwan mutanen da suka bace a cikin baraguzan gini.

A bangare guda kuma sama da mutane 2,500 ne suka rasa gidajensu kamar yadda jami’an ceton suka bayyana.

Girigizar kasar mai karfin maki 6.2 bisa ma’aunin richter da ta aukawa birnin Norcia da ke tsakiyar kasar Italiya yayinda jama’a ke barci ta yanke hanyoyi da dama a yankin.

Wata hukumar binciken kan girgizar kasa ta kasar Amurka ta ce amon girgizar kasar mai karfin maki 5.5 mafi karfi a yankin kamar yadda tarihi ya nuna ya shafi yankunan Lazio da Marche.

Tuni dai gwamnati ta aika da sojoji tare da fitar da kudi euro miliyan 235 domin kai agaji ga wadanda girgizar kasar ta ritsa da su.

A bangarensa kuma Pope Francis ya dage taattakin da ya yi shirya yi domin nuna alhini da kuma addu'o'i ga mutanen da girgizar kasar ta ritsa da su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.