Isa ga babban shafi
Italiya

Jami'an Italiya sun ceto 'yan gudun hijira dubu 3 a teku

Hukumomin Italiya sun sanar da ceto ‘yan gudun hijira sama da 3 da 300 a tekun Mediterranean a karshen makon daya gabata.

Jami'an tsaron Italiya sun ceto 'yan gudun hijira sama da dubu 3 da 300 a tekun Mediterranean
Jami'an tsaron Italiya sun ceto 'yan gudun hijira sama da dubu 3 da 300 a tekun Mediterranean AFP PHOTO/HO/SIRPA/C-G QUILLIVIC
Talla

Mai magana da yawun rundunar sojin ruwan kasar ya ce, jami’an da ke tsaron gabar ruwan ne da hadin gwiwar sojin ruwa suka gudanar da aikin ceto mutanen a wurare daban daban har 26 a gabar ruwan Libya.

Sai dai an tarar da gawar mutum guda daga cikin ‘yan gudun hijrar yayin da hudu daga cikin su suka samu raunuka, inda aka garzaya da zu asibitin tsibirin Lampedusa a cikin jirgi mai sukar ungulu.

Kasar Italiya na cikin kasahesn Turai da suka fi fama da kwararar ‘yan gudun hijira a wannan lokacin da aka bayyana a matsayin mafi muni tun lokacin yakin duniya na biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.