Isa ga babban shafi
NATO

NATO na gudanar da babban taronta a Warsaw

Yau Litinin ake fara babban taron kungiyar NATO ko OTAN a Warsaw, wanda zai kasance babban taro mai muhimmanci tun karshen yakin cacar baka tsakanin Rasha da manyan kasashen Turai.

Yau NATO ke gudanar da babban taronta a Warsaw na Poland
Yau NATO ke gudanar da babban taronta a Warsaw na Poland 路透社
Talla

Masharhanta dai na ta tabo wasu muhimman batutuwa da ake ganin wannan taro zai maida hankali akai.

Daya daga cikin batutuwa da ake ganin ba zai yi wa kasar Rasha dadi ba shi ne batun da Gamuc da Birtaniya da Amurka suka tsayar na tura dakaru kusan dubu 4 zuwa Estonia, Latvia, Lituania da Poland, karkashin inuwar kungiyar NATO.

Shirin wanda zai kasance babban aikin girke dakaru a yankunan tun bayan yakin cacaar bakan, wanda kamar yadda sakataren kungiyar ta NATO ke cewa ba wai ana neman tada zaune tsaye bane a yankin.

Wannan mataki na girke dakarun a dab da Rasha, an tsaida wannan shawara ce domin kwantar da hankulan kasashen NATO, daga dukkan wata barazana da ake masu.

An tsara jibge dakaru cikin shirin ko-ta-kwana akalla dubu 40 da za su fara kai dauki idan akwai bukatar hakan.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.