Isa ga babban shafi
Turkiya

NATO ta goyi bayan Turkiya akan ISIL

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta bayyana goyon bayan ta ga gwamantin Turkiya kan yaki da kungiyar ISIL masu da’awar jihadi bayan wata ganawa ta gaggawa da ya gudana tsakanin bangarorin biyu.

Sakataren tsaron NATO Janarl Jens Stoltenberg
Sakataren tsaron NATO Janarl Jens Stoltenberg Reuters
Talla

A ganawar da aka yi tsakanin wakilan NATO da na kasar Turkiya a jiya Talata, shugaban Turkiya Tayyip Erdogan ya ce ba zai ci gaba da yarjejeniya da ‘yan tawayen kurdawa ba a yayin da ake ci gaba da kai wa kasarsa hare hare.

Sai dai wasu kasashen duniya na kallon sakamakon ganawar a matsayin koma-baya ga yarjejeniyar da Turkiya ta riga ta soma da mayakan Kurdawa.

Turkiya dai ta kaddamar da hare hare akan ISIL da ‘yan tawayen Kurdawan a karshen mako sakamakon munanan hare haren da ake ta kai wa a cikin kasar da ya hallaka mutane da dama.

NATO ta bayyana goyon bayan ta ga Turkiya tare da sukar duk wani ayyukan ta’adanci a ciki da wajen kasar.

kasar Turkiya ce ta bukaci wannan ganawar ta musanman da NATO bayan munanan hare haren baya bayan nan da ta daura nauyin akan kungiyar ta ISIL.

Turkiya ta amince da bukatar Amurka na kafa sansaninta a arewacin Syria domin ba ta damar amfani da sarrarin samaniyarta wajen dakile ayyukan kungiyar ISIL da ta mamaye Syria da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.