Kurdawa sun kalubalanci hare-hare da Turkiya ke kaiwa Iraqi da Syria
Shugabannin Kurdawa da ke Iraqi sun yi allawadai da Matakin da Turkiya ta dauka, na kaddamar da hare-hare a kasashen Syria da Iraqi kan mayakan Jihadi, inda ta ce ba zai haifar da zaman lafiya ba.
Wallafawa ranar:
A yau Assabar Sojojin Turkiya sun cigaba da kai hare-haren sama dana artilary kan mayakan ISIL da ke Syria da kuma na kurdawa a arawecin Iraqi, bayan gwamnatin Turkiya ta lashi takobin sanya wando kafa guda da mayakan Jihadi da ke neman zama babban barazanar a kasarta.
Tun dai a safiyar Jiya Juma’a ne sojojin turkiya suka kaddamar da harin farko kan mayakan, inda suka ce baza suyi kasa a gwiwa ba, wajen kare kasar su dama iyakokinta da ke akwai da syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu