Isa ga babban shafi
Turkiyya

Kasar Turkiyya na ci gaba da luguden wuta kan mayakan IS da na PKK

Yau Asabar dakarun kasar Turkiyya sun ci gaba da luguden wuta ba kakkautawa ta sama, kan wuraren dake hannun mayakan IS a kasar Syria.

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan
Talla

Cikin daren jiya Juma’a, dakarun sun kuma yi ruwan bama bamai a kan yankuna 7, dake hannun mayakan Kurdawa dake arewacin kasar Iraqi.
Wannan na zuwa ne bayan wasu hare haren da aka kai cikin wannan makon a cikin kasar ra Turkiyya, da kuma mahukuntan kasar ke dora alhakinsu kan kungiyoyin IS din da PKK ta Kurdawa a Iraqi.
Kanfanin dillacin labarun kasar yace jiragen yakin, kirara F16 sun trashi daga sansaninsu dake birnin Diyarbakir, suka kai harin suka kuma koma lafiya.
A halin da ake ciki kuma, jami’an tsaron kasar ta Turkiyya sun kama kusan mutane 600 da ake zargi ‘yan kungiyoyin IS da PKK ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.