Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiyya na ci gaba da kokarin kwato dreban jirgin saman da ISIL ta kama

Kasar Jordan tace tana yin dukkan abinda ya wajaba, domin kubutar da matukin jirgin saman kasar dake hannun ‘yan kungiyar ISIS, bayan ganin wani hoton video da kungiyar ta fitar, inda ta nuna yadda aka guntule kan wani dan jarida dan kasar Japan, dake hannun ‘yan kungiyar ta ISIS.Wata sanarwa da Sarkin Jordan, Abdalla na biyu ya fitar, ta bayyana cewa kasar na dukkan abinda ya dace don ganin an kubutar da Maaz Kassasbeh, wanda yake hannun ‘yan kungiyar ISIS tun watan December daya gabata.Sanarwar na cewa Jordan tayi iyakacin kokarin ceton Kenji Goto, dan jarida na kasar Japan da aka karas da fille kansa jiya, daga hannun ‘yan kungiyar ta ISIS.Fraiministan Japan Shinzo Abe ya bayyana kisan dan jaridar da cewa wawanci ne, kuma ba zasu yafe ba.Dan jarida Goto ya kasance na biyu dan kasar Japan da kungiyar ta ISIS ta fille kansa a dan tsakanin nan.Shi wannan dan kasar Jordan Maaz Kassasbeh, mai shekaru 26, kamashi ‘yan kungiyar ISIS sukayi a lokacin da jirgin sama da yake tukawa ya rikito yankin da suke.Kasar Jordan dai na cikin kasashen larabawa da suka hada kai da Sojan Amurka, dana nahiyar Turai don yakar kungiyar ISIS.  

Wasu 'yan kasar Jordan suna zanga zangar neman sakin matukin jirgi Maaz Kassasbeh
Wasu 'yan kasar Jordan suna zanga zangar neman sakin matukin jirgi Maaz Kassasbeh REUTERS/Muhammad Hamed
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.