Isa ga babban shafi
Turkiya

An raunata 'yan sanda Turkiya 11 a lardin Diyarbakir

Akalla ‘yan sanda turkiya 11 ne, suka samu munanar raunika a wata arangama da ya afku, tsakanin su da masu zanga-zangar adawa, da hukunci da aka yankewa tsohon shugaban kasar Masar Muhammad Morsi a yankin kuradawa da ke kudu maso gabashin kasar. a yayyin da  'yan sanda ke kokarin tarwatsu ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye.

Masu zanga-zanga a Turkiya
Masu zanga-zanga a Turkiya
Talla

Gwamna Lardin Diyarbakir, ya tabbatarwa kamfanin dilanci labaran faransa AFP cewa, masu zanga-zangar sunyi cuncurundo ne a gaban babba masallacin yankin inda suka shirya tsaf domin gudanar da zanga-zanga a kewayen Diyarbakir.

Masu zanga-zangar dai sun hada da Mabobin Islama da Huda-par da ke da alaka da Hezbollah, da kuma kungiyoyin masu zaman kansu na musulmai, inda suka duga amfani da duwatsu wajen jifa Jami ‘an tsaro, abin daya haifar da arangama tsakanin su da 'yan sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.