Isa ga babban shafi
Turkiya-Masar

Turkiya ta bukaci a sako Mursi

Kasar Turkiyya ta ce, ba zata ci gaba da hulda da kasar masar ba, har sai an sako hambarar shugaba kasar Muhammad Morsi daga gidan yari, da kuma soke hukuncin da aka yankewa wasu magoya bayan sa na daurin rai da rai.

Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyib Erdogan
Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyib Erdogan REUTERS/Henry Romero
Talla

Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyib Erdogan ya bayyana haka a matsayin hanyar da kasashen biyu zasu sake dawo da hukdar dake tsakanin su.

Alaka tsakanin kasashe biyu dai ya gamu da matsala, tun bayan karbe ragamar mulki kasar da Abdel Fatah al-sisi yayi, bayan hambarar da zabeben shugaba Muhd Morsi acikin shekarar ta 2013.

Lamarin dai ya haifar da zanga-zanga tsakanin kungiyoyin ‘yan uwa musulmi, inda jami’a tsaro suka bude musu wutar da yayi sanadin mutuwar da daman daga cikinsu a birnin Alkahira, yayyin da aka kame wasu aka daure cikin su harda tsohon shugaban Morsi da wasu jiga-jigai a gwamnatin sa.

Shugaban Kasar Turkiya Tayyib Erdogan ya ce Morsi zababen shugaba ne, da ya samun yawan kuri’u, kaso 52 cikin 100, don haka ya can-canci a bashi cikaken yancin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.