Isa ga babban shafi
Rasha

Putin ya soki NATO

Shugaban Kasar Russia Vladimir Putin ya yi mummunan suka kan kungiyar kawancen tsaro ta NATO dangane da yadda take ruruta wutar yaki a kusa da iyakar kasar, tare da yin gargadin cewar kungiyar na tilsatawa Rasha shiga damara.

Shugaban Rasha Vladimir Putin da Ministan tsaro Sergei Shoigu a bikin cika shekaru 71 na samun nasara akan dakarun Nazi
Shugaban Rasha Vladimir Putin da Ministan tsaro Sergei Shoigu a bikin cika shekaru 71 na samun nasara akan dakarun Nazi ©
Talla

Shugaba Vladimir Putin wanda ya ke jawabi a gaban ‘yan majalisun kasar kan bikin cika shekaru 75 da mamayar da Rasha ta yi wa Jamus, ya ce kungiyar NATO na takalar kasar ta hanyar cacan-baki kusa da iyakar ta, kuma hakan zai ba kasar damar shiga damara don inganta matakan tsaron kasar.

Shugaba Putin ya kuma zargi kasashen Yammacin duniya da watsi da bukatar kasar na hadin-kai don yaki da ta’addanci a duniya, kamar yadda a baya suka yi watsi da gargadin da kasar ta yi kan barazanar Hitler, saboda kyamar da suke wa Rasha kan rikicin kasar Ukraine.

Dangantaka tsakanin Rasha da kasashen Yammacin duniya ta yi tsami tun bayan da sojojin kasar suka kutsa kai cikin Crimea da kuma rawar da kasar ke takawa na goyan bayan masu neman raba Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.