Rasha ta soma janye dakarunta daga Syria
A yau talata ne dakarun kasar Rasha dake taimakawa shugaba Bashar Al-assad na Syria yakar ‘yan ta’adda suka soma janyewa daga kasar bisa umarnin shugaba Vladimir Putin
Wallafawa ranar:
A daren jiya ne shugaba Vladimir Putin ya sanar da bukatar kasarsa na janye dakarunta daga Syria, kamar yadda dai aka ji labarin shiga yakin kwatsam a farko haka aka ji labarin janyewarta daga Syria, bayan watanni 4 da Rasha ta kwashe tana luguden wuta akan mayakan jihadi da suka hana zaman lafiya a Syria
Mr Putin wanda ya sanar da matakin janye dakarun yace hakan shine daidai ganin haka ta cimma ruwa a kokarin Rasha na tarwatsa kungiyoyin ‘yan ta’dda
Yanzu haka ma dai tawagar Majalisar Dinkin Duniya da bangarorin dake rikici da juna a Syria sun koma zaman tattauna hanyoyi kawo karshen rikicin na Syria a birnin Geneva
Shekaru sama da 4 aka kwashe ana fama da tashe tashen hankula kuma mutane sama da 300,000 ne suka rasa rayukansu baya ga miliyoyi da suka tsere daga muhallinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu