Isa ga babban shafi
Syria-Amurka-Rasha

Amurka da Rasha sun kulla yarjejeniyar tsagaita wutar Syria

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yaba da yarjejeniyar tsagaita wuta da kasashen Amurka da Rasha suka cim ma a kan rikicin Syria tare da yin kira ga bangarorin da ke rikici su amince da kuma yin aiki da yarjejeniyar don kawo karshen rikicin kasar da ya lakume rayukan dubun dubatar mutane.

Sakataren Harakokin wajen Amurka John Kerry  da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov suna tattauna batun Syria
Sakataren Harakokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov suna tattauna batun Syria REUTERS
Talla

Amurka da Rasha ne suka sanar da cim ma yarjejeniyar wacce zata soma aiki a ranar Assabar tsakanin bangaren gwamnatin Bashar Al Assad da kuma ‘yan adawa da ke fada da dakarun shi.

Sai dai yarjejeniyar ba ta shafi mayakan da ke da’awar jihadi ba a kasar ta Syria da suka hada da mayakan IS.

Ban ki Moon ya ce cim ma yarjejeniyar alamu ne da ke nuna samun nasara musamman ga mutanen Syria bayan shafe shekaru 5 ana gwabza fada.

Majalisar Dinkin Duniya tace idan har bangarorin na Syria suka mutunta yarjejeniyar, to za a samu damar shigar da kayan jin kai ga dimbin makubakata da rikicin kasar ya jefa cikin mawuyacin hali na yunwa.

An dai shafe lokaci mai tsawo manyan kasashen duniya na kokarin shawo kan rikicin Syria wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da rabin miliyan tare da tursasawa Miliyoyan barin kasar.

Rasha da Amurka da suka taka rawa wajen cim ma yarjejeniyar, shugabannin kasashen sun tattauna ta wayar tarho kan sharuddan da za a aiwatar da yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.