Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya na goyon bayan farmaki a Syria

Gwamnatin Turkiyya ta ce tana goyon bayan yin amfani da sojojin kasa domin kai farmaki a cikin kasar Syria matukar dai kasashen kawance suka amince da daukar irin wannan mataki.

Kasar Syria na fama da tashe-tashen hankula
Kasar Syria na fama da tashe-tashen hankula DR
Talla

Wani babban jami’in gwamnatin Turkiyya ne wanda bai amince a bayyana sunansa ba, ya sanar da haka a daidai lokacin da manzon Majalisar dinkin duniya a Syria Staffan de Mastura ke cewa gwamnatin Assad ta amince a tura kayayyakin agaji zuwa birane 7 da aka yi wa kawanya.

To sai dai a jawabin da ya gabatar a cikin daren da ya gabata, jagoran kungiyar Hizbullah a Lebanon kuma daya daga cikin wadanda ke mara wa Bashar al-Assad a wannan yaki, Hassan Nasraallah, ya zargi Saudiyya da Turkiyya da jefa yankin gabas ta tsakiya a halin kaka-nikayi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.