Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya na zaben raba gardama kan Tarayyar Turai

Miliyoyin mutanen Birtaniya sun soma kada kuri’ar raba gardama da zata tabbatar da zaman kasar cikin kungiyar kasashen Turai ko kuma ficewarta daga kungiyar da aka kafa shekaru 60 da suka gabata.

Mutanen Birtaniya na zaben raba gardama kan ficewa Tarayyar Turai
Mutanen Birtaniya na zaben raba gardama kan ficewa Tarayyar Turai REUTERS/Neil Hall
Talla

Mutane miliyan 46 da rabi ake sa ran su kada kuri’a a zaben da tuni ya raba kan al’ummar kasar tare da haifar da gaba da sukar juna har ma da rasa rayuka, yayin da kasashen duniya da dama da hukumomi dabam dabam ke jan kunne Birtaniya da ta dauki matakin da ya dace ko kuma ta fuskanci mawuyacin hali.

Rahotanni sun ce ruwan sama da aka tafka a kudu masu gabashin London bai hanawa mutane isa ga runfunan zabe ba domin kada kuri’arsu a zaben da zai tantance makomar Birtaniya.

Sakamakon jin ra’ayin jama’a na karshe da aka gudanar ya ba masu son kasar ta ci gaba da zama a Tarayyar Turai nasara da kashi 48 fiye da wadanda ke son ficewar Birtaniya da suka samu kashi 42.

Amma wasu kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar kafin soma zaben ya nuna masu son ficewa ne kan gaba, amma da kashi guda ko biyu na yawan kuri’u, wanda ke nuna zaben raba gardamar kamar “mace mai ciki ce”.

An shafe tsawon watanni hudu ana gudanar da yakin neman zabe kan zaben na raba gardama, inda aka gudanar da zazzafan yakin neman zabe a game da wannan batu tsakanin magoya baya da kuma masu adawa da ci gaba da kasancewar Birtaniya a cikin kungiyar Turai.

Masu fatan ganin kasar ta fice daga kungiyar kamar Boris Johnson da kuma Nigel Farage, sun ce lokaci ya yi da al’ummar kasar za su yi imani da kasarsu, bayan shekaru 40 a cikin kungiyar.

Matukar dai masu fafutukar ficewa daga wannan gungu suka yi nasara a zaben na yau, to wannan zai kasance karo na farko da wata kasa ta balle daga Tarayyar ta Turai, lamarin da zai haifar da samako maras kyau ga tattalin arzikin Birtaniya kamar dai yadda masana suka yi hasashe.

Sai dai shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-claude Juncker, ya ce ba ya fata hakan za ta faru, yana mai yin kira ga al’ummar Birtaniya da su zabi kasancewa tare da sauran ‘yan uwansu na yankin Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.