Isa ga babban shafi
Birtaniya

An tafka muhawara kan ficewar Birtaniya daga Turai

Bangarorin da ke adawa da juna kan matsayin Birtaniya na ci gaba da zama ko kuma ficewa daga kungiyar kasashen Turai sun tafka muhawara mai zafi, inda suka yi kokarin janyo hankalin masu kada kuri’u don ganin sun samu nasara.

A gobe Alhamis ne al'ummar Birtaniya za su kada kuri'ar raba gardama kan ci gaba da zama ko kuma ficewa daga kungiyar tarayyar Turai
A gobe Alhamis ne al'ummar Birtaniya za su kada kuri'ar raba gardama kan ci gaba da zama ko kuma ficewa daga kungiyar tarayyar Turai REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Tsohon magajin garin birnin London, Boris Johnson ya bayyana zaben na gobe a matsayin lokacin samun 'yancin kan Birtaniya muddin aka zabi ficewa daga Turai, yayin da Sadiq Khan, sabon magajin garin na London ya zargi Boris da karya wajen shaida wa 'yan kasar cewa, kasar Musulmai wato Turkiya za ta shiga kungiyar Turai ta kuma mamaye ta, inda ya yaba da rawar da baki suka taka wajen gina Birtaniya.

A bangare guda kuma Firaministan Birtaniya David Cameron ya bukaci al’ummar kasar da su yi nazari kan makomar ‘ya’yansu da tattalin arzikin kasar, kafin su kada kuri’ar ficewa daga kungiyar ta tarayyar Turai.

Mr.Cameron ya gargadi cewa, al’ummar da za su zo nan gaba da kuma tattalin arzkin kasar za su shiga cikin tsaka mai wuya da zaran kasar ta zamo ta farko da ta fara ballewa daga Turai.

A cewar Cameron, za su fi samun karfi idan suka ci gaba da zama, idan kuma suka fice, to lallai za su yi rauni sosai, abinda ya danganta da babbar barazana ga daukacin kasar.

Fitaccen attajiran nan mai tallafa wa jama’a, George Soros ya yi hasashen cewa, darajar kudin Pam na Birtaniya za ta fadi a ranar jumma’a mai zuwa mtaukar kasar wadda ita ce ta biyar wajen karfin tattalin arziki a duniya, ta amince ta ware kanta.

Mr. Soros ya kara da cewa, a tashin farko darajar Pam din za ta fadi da fiye da kashi 15 cikin 100.

Sai dai masu goyon bayan ci gaba da zaman Birtaniya sun yi watsi da kalaman Soros inda suka ce, shi ma yana son a gina Turai ne kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.