Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya za ta tsawaita rijistar masu zaben raba gardama

Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta tsawaita lokacin rijistar masu kada kuri’a a zaben raba gardama da za a gudanar domin ficewar kasar daga Tarayyar Turai, wannan kuma na faruwa ne sakamakon tangardar da na’urar yin rijistar ta samu.

Firaministan Birtaniya David Cameron
Firaministan Birtaniya David Cameron chris lobina / SKY NEWS / AFP
Talla

Wasu kasashen yankin gabacin Turai sun yi kira ga Birtaniya ta yi watsi da kudirin ficewa daga Tarayyar Turai

Birtaniya za ta kara wa’adin yin rijistar masu kada kuri’ar ne na tsawon sa’o1 48.

Wannan kuma na faruwa ne sakamakon tangardar da aka samu a shafin intanet da ake yin rijistar saboda yadda mutane suka yi wa shafin yawa a lokaci guda.

A yau Alhamis majalisa za ta tattauna amincewa da tsawaita wa’adin da ya kawo karshe a daren Talata, a yayin da ya rage makwanni biyu a kada kauri’ar ballewar Birtaniya daga Tarayyar Turai a ranar 23 ga watan Yuni.

Rahotanni sun ce mafi yawancin wadanda suka yi rijistar matasa ne masu kananan shekaru, wadanda kuma ake ganin zasu kada kuri’ar amincewa da kasancewar Birtaniya a Tarayyar Turai.

Wasu dai sun yi zargin an shirya magudi ne domin yi wa masu goyon bayan ficewar Birtaniya daga Turai rijista.

Firaministan kasar David Cameron ne dai ya bullo da matakin jefa kuri’ar domin ballewa daga Turai.

Kasar Holland ta yi gargadin cewa tattalin arzikinta zai tabu matuka idan har Birtaniya ta fice daga kungiyar Turai.

Holland ta yi kiyasin cewa ci gabanta zai ragu da sama da kashi 1.2 daga nan zuwa 2030.

Kasashen gabashin Turai da suka hada da Poland da Jamhuriyyar Czech da Hungary da Slovakia sun bukaci Birtaniya ta yi watsi da shirin ficewa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.