Isa ga babban shafi
Birtaniya

Ana ci gaba da alhinin mutuwar Cox a Birtaniya

Al’ummar duniya daga sassa daban daban na ci gaba da mika sakon ta'aziya kan mutuwar ‘yar majalisar dokokin Birtaniya Jo Cox, wadda ta rasa ranta bayan wani mutun ya harbe ta da bingida sannan kuma ya daba ma ta wuka.

Masu nuna alhini na ajiye furanni don girmama marigayiya Jo Cox
Masu nuna alhini na ajiye furanni don girmama marigayiya Jo Cox 路透社
Talla

An dai kashe Cox ne mai shekaru 41 kuma ‘yar jami’yyar Labour bayan ta kammala wata ganawa a Birstall da ke kudancin Yorkshire a ranar Alhamis.

Uwargida Hilary Clinton da ke neman tsayawa takarar shugabancin Amurka karskashin jam’iyyar Democrat na daga cikin wadanda suka aike da sakon ta’aziya don girmama marigayiyar.

Mrs. Clinton ta bayyana kaduwarta kan mutuwar Cox, wadda ta ce, an kashe ta cikin wani yanayi na zalunci da rashin tausayi.

Rahotanni sun ce, a lokacin da ya ke aikata kisan, maharin ya yi ta fadin cewa, “ a rika sanya manufar Birtaniya a gaba” kuma ya fadi haka akalla sau biyu.

Tuni dai aka cafke wani mutum mai shekaru 52 da ake zargi da kisan.

Mrs. Cox na daga cikin masu goyon Birtaniya da ta ci gaba da zama a cikin kungiyar kasashen Turai a maimakon ficewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.