Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Ukraine ta yi barazanar kaddamar da halaltaccen yaki kan Rasha

Kasar Ukraine ta yi barazanar kaddamar da abinda ta kira, halaltaccen yaki a kan makwabciyarta kasar Rasha, bayan hukumomi a birnin Moscow sun amince da wata sabuwar yarjejeniyar da za ta iya yiwa Ukraine kafar ungulu, game da shirin yafe mata bashi da wasu kasashe ke yi.

Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko
Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko REUTERS/Andrew Kravchenko/Pool
Talla

Tuni dai gwamnatin Ukraine, ta bai wa Rasha wa’adin nan da ranar 29 ga wannan wata, da ko dai ta amince da sabbin ka’idojin da sauran kasashe suka amince da su ko kuma ta gurfanar da ita a gaban kotun duniya.

Firaministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk, ya bayyana cewa mafi yawan kasashe da kungiyoyi masu bada lamani na duniya, sun amince su yafe wa kasar fiye da kashe 75 na bashin da suke bin ta.

Fira Minista Yatsenyuk, ya ce yarjejeniyar za ta bai wa kasar damar cin gajiyar yafiyar bashin Dala biliyan 3 a nan take.

A watan Agusta ne Ukraine, ta cimma yarjejeniya da wasu manyan kamfanonin zuba jarin kasashen yammacin duniya su 4 wadanda sune masu binta sama da Dala biliytan 18, inda suka amince da bata tallafi tare da sassauta ka’idojin biyan bashin.

Sai dai kuma Rasha ce ka dai daga cikin manyan kasashen da ake neman goyon bayansu kan shirin, ta ki bada goyon bayanta.

Kasar ta Rasha tana shirye shiryen karar Ukraine a gaban wata kotu a London wadda ke da hurumin ayyana Ukraine a matsayin kasar da ta samu karayar tattalin arziki, lamarin da zai iya sanyaya guiwowin kasashen dake kokarin tallafa wa Ukraine din.

Ana sa ran nan gaba asusun bada lamani na duniya wato IMF, zai sa baki game da wannan cacar baki da ta kaure tsakanin kasashen 2 makwabtan juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.